Skip to main content
HausaRadio.net

HausaRadio.net

By HausaRadio.net

Available on
Apple Podcasts Logo
Castbox Logo
Google Podcasts Logo
Overcast Logo
Pocket Casts Logo
RadioPublic Logo
Spotify Logo
Currently playing episode

"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao

HausaRadio.netMay 24, 2021

00:00
16:12
"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao

"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao

Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao


Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka da yawan su, sun gwammace su yi hijira zuwa arewa.


Podcast Trailer: https://youtu.be/qzLb2V9521U

May 24, 202116:12
Komai muka samu mu fassara zuwa yaren mu Hausa - Malam Habibu Sani Babura

Komai muka samu mu fassara zuwa yaren mu Hausa - Malam Habibu Sani Babura

Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa  a Jami'ar Bayero ta Kano.

Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna Firdausi).

Sep 04, 202003:28
#RanarHausa 2020-08-25 Arewa Radio 93.1's Program with BANNigeria
Aug 25, 202052:35
#RanarHausa 2020 - Shirin Daga Taskar Hausa Daga Guarantee Radio 94.7 Kano
Aug 24, 202039:26
Kaucewa #LabaranBogi (Stopping the spread of #FakeNews in Hausa media)
Jul 25, 202022:20
Asalin Ranar Hausa 2015 - Shirin VOA Hausa na Yau Da Gobe
Jul 25, 202019:06
DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28

DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28

DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28

Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda

May 28, 202009:40
Hausa News Headlines - Kanun Labaran Hausa na 2020.05.08
May 09, 202005:03
BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22

BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22

Show notes and transcript <> Cikakken bayanin wannan podcast din: http://bit.ly/BBCHausaSafe20190522

May 22, 201901:40
RFI Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin 07h00 Asabar 2019.05.18
May 18, 201901:16
VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri

  1. US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka.
  2. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya.
  3. Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel... Read more at http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517
May 18, 201901:51
BBC Hausa News Headlines  Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17
May 17, 201901:35
DW Hausa Shirin Safe na 2019-03-01

DW Hausa Shirin Safe na 2019-03-01

DW Hausa Shirin Safe 01.03.2019 [1]

Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin.

  1. Hosts: Muntaqa Ahiwa
  2. Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke fama da matsaloli.
  3. Cameroon: Yara ne da ke fama da cutar nan ta HIV mai karya garkuwar jiki da ke cikin mummunar yanayi na rashin maganin rage raɗaɗin wannan cuta.
  4. Senegal: Zaɓen da aka kammala.
  5. North Korea: Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin sake zama da Amurka bayan tashi taron birnin Hanoi da aka yi ba tare da wata nasara ba.
  6. Amurka ta taya Najeriya murnar kammala zaɓe cikin kwanciyar hankali.
  7. Somalia: Wani harin ƙunar baƙin wake, ya salwantar da rayuka a ƙasar Somaliya.
Mar 01, 201901:20
ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019)

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019)

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Abdullahi Salihu*
  2. Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar.
  3. Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha, da kuma abubuwan da taron ya cimmawa game da yiyuwar aiwatar da su a aikace.
  4. France: Za mu duba batun matakan da sojojin gwamnatin ƙasar France suka ɗauka na kare wanda ya juya mulki da suka ce an yi yunƙurin aiwatarwa a ƙasar Cadi.
  5. Iran, Lebanon: Za a ji sharhin [ unintelligible: bayan labaran? ] wadanda suka yi magana akan ziyarar wadansu harkokin wajen Iran a ƙasar Lebanon.
  6. Shirin Ko Kun San, Kaza a kan dame, shirin labaran wasannin mako.
  7. Venezuela: Shugaban ƙasar Venezuela ya ce ƙasar za ta zamai wa Amurka Vietnam matuƙar ta kai mata hari.
  8. Bahrain: An cika shekaru takwas da fara yunƙurin al'umma a ƙasar Bahrain.
  9. China: ƙungiyar kare hakkin bil Adama (human rights) na ƙasashen duniya sun zargi ƙasar China da take hakkokin musulmi.
Feb 14, 201903:04
BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Sulaiman Ibrahim Katsina
  2. Nigeria Elections 2019:
    1. A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar.
    2. Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau.
    3. Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a."Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (11:30) na bar gida na. Na tattara kayana, na zo na zauna. Zan yi alƙawari kwana uku.
  3. EU: Tarayar Turai ta kammala wani tsari na wata doka, wadda ta shafi haƙƙin mallaka a intanet. Sai dai, akwai masu ƙorafi akan haka. Za mu ji ko su wanene.
  4. Labarin wasanni (sports).
Feb 14, 201901:07
BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. Liberia: In gano gawar mutane biyar amma a mahaƙar ma'adinai ta gwal wadda ta rifta a arewacin Liberia a makon da ya wuce.
  3. USA, Yemen: 'Yan majalisar Amurka sun gabatar da uzurin da zai janyowa dakarun ƙasar su janye daga Yemen.
  4. Nigeria Elections 2019: Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaɓe a Najeriya, masu larura ta musamman na ƙorafi kan jami'an tsaro a rumfunan zaɓe."Dubu biyu da sha biyar (2015), na je zan jefa ƙuri'a na, aka ce min ni in bi layi domin ban fi kowa ba. A bisa ga kundin tsarin dokoki na hukumar zaɓe. Mu akwai kulawa ta musamman. Idan muka zo, ba za mu bi layi ba.
  5. Sports: Real Madrid ta doke Ajax (Ayax) da ci biyu da ɗaya (2-1). Wasan farko, zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarin Turai. Sai kuma ana fara yabawa mai horasda Madrid ɗin.
Feb 14, 201901:19
BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru.
  3. Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma, ana ta ɓangaren, APC ta musanta wannan zargin: "Na farko dai, fili na gwamnati ne kuma na tabbata akwai ƙa'idoji wadda ake bi. Maganar cewa wai yau an hana su taro domin wani abu... tsoron faɗuwa ne, shi ya sa suke neman duk ta hanyar da za'a bi a tayar da hankali."
  4. Sudan: BBC ta bankaɗo wani wuri da ake tsare masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati tare da azabtar da su a ƙasar Sudan.
  5. Taƙaitaccen labarin wasanni.
Feb 14, 201901:26
VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
  2. Nigeria: Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ƙaryata jita-jita da ake yi na cewa jami'an ƙasar basu da kayan aiki."Ko ƙasar America, ko ƙasar Ingila (England), ko ƙasar Russia, ba za su ce suna da isasshun kaya da suka ishe su ba.
  3. Muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC, Ibrahim Mago, ya ce za su gurfanar da masu siyan da ƙuri'a da masu tada fitina lokacin zaɓr a gaban kotu.
  4. Ba shirin Nakasa.
  5. Ghana newspaper headlines <> sharhin jaridun Ghana.
  6. Saƙonnin masu sauraro na kan na'ura.
Feb 14, 201901:12
VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
  2. USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri.
  3. USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga.
  4. USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafin soji da Amurka ke baiwa gamayyar sojojin da Saudiya ke jagoranta a yaƙin Yemen.
  5. Nigeria Elections 2019: Manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya, sun sake jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla.
  6. Nigeria: Gwamnar jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsallake rijiya da baya a ƙauyen Lugumanu*."Mu mun ɗauka sojoji ne, ashe ba sojoji ba ne. Suna da kayan sarki kuma dukansu sun more..."
  7. Ba shirin Domin Iyali.
Feb 14, 201901:37
World Radio Day in Hausa (Ranar Rediyo ta Duniya 2019)

World Radio Day in Hausa (Ranar Rediyo ta Duniya 2019)

  1. RFI Hausa's coverage of World Radio Day (0:00-1:16)
  2. DW Hausa's coverage (1:16-4:54)
  3. BBC Hausa's coverage (4:54-8:49)
Feb 13, 201908:49
DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019) [1][2]

Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba.

  1. Host: Munta Gayuwa*
  2. Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon shekaru da ƙasar ta kama mulki irin na demokraɗiya. Toh wane irin alƙauran ne wadannan 'yan siyasa ke yi wa wadannan mutane na karkara?"In mun ci zaɓe, za mu yi muku hanya. In mun ci zaɓe, za mu kawo muku wuta, asibiti, da sauran abubuwa. Amma ko ɗaya, ba wanda ya taɓa cika mana. Wani pole-waya an kafa a nan ya kai har shekara goma sha biyu (12), amma wallahi ba a zo yin komai ba!"
  3. Nigeria: Muna tafe da rahoto kan wannan matsala. Hakannan kuma za'a ji al'ummar Fulani da dokar hana kiwo ta shafa a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriyar. Sun buƙaci kariya ne daga jami'an tsaro a duk inda suke don basu damar zaɓe kamar sauran 'yan ƙasar Najeriyar.
  4. World Radio Day 2019: Yayin kuma da ake ranar rediyo ta duniya, za mu ji yadda wasu al'ummomi ke bayyana mahimmancin kafarta sadarwa a garesu.
  5. Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco, sun kama wasu Faransawa da suka ce suna ɗaukar nauyin ƙungiyar nan ta IS.
  6. Nigeria: Mutane da dama sun mutu lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.
  7. Thailand: Wasu fursunoni, wato 'yan ƙabilar Uyghir, sun tsere daga hannun jami'an tsaro a ƙasar Thailand.
Feb 13, 201902:01
BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019) [1] [2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta.
  3. Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum.
  4. Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya."Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin tsaro da ya addabi mutane, da yaudara, da sauransu... da aka saba ganin 'yan siyasa suna yi. Wanda mu ba mu fito ba da wannan..."
  5. Cameroon: Za kuma ku ji kiraye-kirayen da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke yi wa hukumomin Kamaru domin su sako wata ɗaliba da ake tsare ita.
Feb 13, 201901:17
BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT)

BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT)

BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT) [1][2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. Venezuela: Shugaban 'Yan adawa a Venezuela, ya sha alwashin shigar da kayan agaji. Duk kuwa da cewa shugaba Maduro ya ƙi amincewa da hakan.
  3. Nigeria: Ana cigaba da cece-kuce kan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Zamfara. Da ake cewa hakan zai iya haddasa fitina. Toh sai dai kuma magoya bayanshi sun ce an yi masa mummunar fahimta.
  4. Shin kuma ko wace rawa ce rediyo ke takawa a rayuwar al'umma? Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin.
  5. Sports: labarin wasanni.


Feb 13, 201901:01
BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT)

BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT)

BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT) [1][2]
  1. Hosts: Aminu Abdulkadir
  2. Sudan: Jami'an tsaron ƙasar Sudan sun tsare wani rukunnin shegunnan malamai na jami'o'i. Da suka yi zanga-zangar ƙin jinin shugaba Umar Al-Bashir a Khartoom - babban birnin ƙasar.
  3. Nigeria: Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu mutane dangane da gobarar da tashi a wani ofishin hukumar zaɓe, yau a jihar Anambara. Gobarar ta haddasa ɓarna."Toh, har yanzu dai ba mu kai ga tantance yawan adadin wannan na'uran, ko guda nawa ne suka ƙone ba. Amma dai sun kashe tamanin da biyar cikin ɗari (85/100) sun ƙone.
  4. DRC: 'Yan sanda sun tabbatar da kama mutane goma sha biyar dangane da rikicin ƙabilancin da ya haddasa mutuwar ɗarurwan mutane.
  5. Sports <> Labaran wasanni.
Feb 13, 201901:48
BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG) [1][2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. India: 'Yan sanda Indiya sun ce mutane sha bakwai ne suka mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Delhi.
  3. Haiti: Masu zanga-zanga sun yi ta ƙona tayoyi a titunan ƙasar Haite tare da jefan jami'an tsaro da duwatsu.
  4. Nigeria: Wasu 'yan Najeriya sun ce sun gaji da alƙawarin da gwamnati ke musu na bunƙasa harkar sufurin jirgin ƙasa a sassan ƙasar."Muna jin daɗin yanda aikin kasancewa. Amma kuma abinda muke gude shine, kada yazo ya kasance kamar aikin bayan ya fara kuma a tsaya. Sabida, sun san abu kamar za su yi, za su yaudari mutane. Can kuma, su yi amfani da kuɗin su yi wani abu."
  5. Labarin wasanni <> sports.
  6. Nigeria Elections 2019: Za ku ji zargin da jam'iyyar APC da PDP ke yi kan kawowa juna hare-hare gabannin zaɓen da ke tafe a Najeriya.


Feb 12, 201901:18
Kanun Labaran BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG)

Kanun Labaran BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG)

BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG) [1] [2]
  1. Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
  2. USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka.
  3. Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar."I beleive our military are not getting the best of equipment... <> Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za ka ga makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su, sun fi na sojoji inganci da zamunanci."
  4. Election special: Sashen Hausa na BBC sun yi tanadi na musamman a lokacin zaɓen."Saboda idan ka fara shiri, ba za ka tsaya ba, tun ƙarfe shida na safe (6 AM), har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Ɗanɗanon shirin da sauran shirin zai sauya, kamar yadda muka sauya shi a lokacin da muka yi bakukuwan cika shekaru sittin da kafuwa."
Feb 12, 201901:36
DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 Headlines

DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 Headlines

DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 [Cikakken Shirin / Full broadcast]

Za ku ji cewar kasar Turkiya tayi Allah wadai da irin cin zarafin da kabilar Uighur ke fuskanta a kasar Chaina

  1. Host: Zulaiha Abubakar Kibiya
  2. African Union: Ƙungiyar tarayyar Afika ta AU, za ta gudanar da babban taron ta na kwanaki biyu a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha (Ethiopia) inda shugwabannin ƙasashen Afrika za su tattauna batun kwararar baƙin haure daga nahiyar zuwa ƙasashen turai.
  3. Daidai lokacin da a cigaba da lalubo dabarun warware rikicin addini da ƙabilanci da ke barazana da rayuwar al'umar Filato.
  4. Cibiyar sasanta tsakanin addinai mai ofishi a Kaduna, ya ƙaddamar da shirin yafewa juna tsakanin al'ummomin jihar bayan shafe sama da shekaru goma sha bakwai ana tashin hankali.
  5. Shugaba Paul Kagame zai sauka daga muƙaminsa a ƙungiyar AU.
  6. An shawarci sojojin ƙasar Venezuela a kan kayan agaji.
  7. Turkiyya ta yi Allah-wadai da cin zarafin da ƙabilar Uighur ke fuskanta China.
Feb 10, 201901:26
BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019 [14]

Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.

  1. Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
  2. Turkey, China: Turkiyya ta buƙaci ƙasar Sin da ta gaggauta ta rufe sansanonin da take tsare musulmi 'yan ƙabilar Uyghur.
  3. UK: Yarima Philip na Birtaniya ya ajiye lasisinsa na tuƙi.
  4. Nigeria's corn farmers: Manoma masara sun bayyana irin yabon da suka ce sun samu a noman bara.Mun samu cigaba wajen bunƙasuwan masara daga shekara ta dubu biyar da sha biyar zuwa yanzu (2015-present). Da, masarar da ake nomawa a wannan lokaci ba ta wuce tonne miliyan sha biyar ba. Amma yanzu zuwa bana, noman da aka yi na bara shekara ta dubu biyu da sha takwas (2018), an noma ta miliyan ashirin.
  5. Shirin Mu Tattauna.
Feb 10, 201901:04
BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019 [12]

Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.

  1. Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin
  2. Nigeria Elections 2019 / Zaɓe 2019: APC! APC! Today I want to teach Atiku a lesson.--Uban jam'iyyar APC Bola Ahmed Tunibu a yayin yaƙin neman zaɓen jihar Lagos ya ke cewa yau zan koyawa Atiku darasi. Za mu ji me yayi zafi da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya kasance.
  3. Sokoto Governor Debate: A yau BBC ke cika alƙawarinta na kawo muku mahawara tsakanin 'yan takaran gwamnan Sokoto.
  4. Africa: Shugwabannin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afrika za su soma wani taro da zai mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi nahiyar su.
Feb 10, 201901:22
BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019

BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019

BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019 [10][11]

Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.

  1. Hosts: Ibrahim Mijinyawa
  2. Nigeria Elections 2019: Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP (the major opposition party), ta yi zargin cewa an hana ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a Abuja.Har mun tura mutanen mu waɗanda za su je su shiya mana wurin tsayawa a yi magana (podium)... sai aka ce musu wannan wuri ba za a ba mu shi ba. Don haka sai dai mu nemi wani.
  3. Chad: Rundunar sojin Cadi kuwa, ta ce ta kama 'yan tawaye da dama da suka tsallaka cikin ƙasar daga kudancin Libya bayan artabun da aka yi da su a arewacin ƙasar.
  4. Ethiopia: Tsofaffin 'yan tawaye ne sama da dubu guda suka miƙa da makamansu bayan wata yarjejeniya da aka ƙulla da su da gwamnatin ƙasar.
Feb 10, 201901:26
Pars Hausa Sunday, Feb 10th 2019

Pars Hausa Sunday, Feb 10th 2019

Pars Hausa Sunday, Feb 10th 2019 [8][9]
  1. Hosts: Aminu Abdu
  2. Niger: The Minister of State for the Interior Mohamed Bazoum ya jagoranci wata tawaga da ta haɗa da 'yan majalisu da manyan jami'an ƙasar zuwa garin Adze* na cikin gwadomar Abalak da ke jihar Tahoua domin tattaunawa da al'ummar yankin kan abinda ya shafi harkokin tsaro da zaman lafiya na yankin.
  3. Nigeria: Rahotanni sun tabbatar da cewa wata gobara ta rutsa da wasu 'yan gudun hijira a sansanin Munguno, Borno. Za'a ji ra'ayin masana dangane da wannan lamari.
  4. Nigerians living in Cote D'voire: 'Yan Nijar da ke rayuwa a ƙasar Cote D'voire sun koka kan yadda suke samun matsala da katin ɗan ƙasa. Ganin cewa muhukuntan na Niger sun ƙi sabunta katin da ta yi daidai da zamani. Lamarin da ya sanya suke fuskantar matsala na gudanar da mu'amalarsu a ƙasar ta Cote D'voire.
  5. Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco sun sanar da janyewar ƙasar daga cikin gurundunar ƙawancen Saudiya a ƙasar Yemen tare da kiran jakadan ƙasar daga birnin Riyadh. Ko me hakan ya ke nufi, za mu ji ra'ayin masana.
  6. Shirin Ko Kun San da Tahir Amir Rajiyola*.
  7. Shiri na musamman (Special Report) dangane da zagayowar ranar nasarar juyin-juya halin Musulunci na Iran.
  8. Shiri na Matambayi Baya Ɓata da Muhammad Auwwal Bauchi.
Feb 10, 201901:45
BBC Hausa - Shirin Rana na 07.02.2019

BBC Hausa - Shirin Rana na 07.02.2019

Host: Sulaiman Ibrahim Katsina


  1. Jiragen yaƙin Faransa sun kai sabbin hare-hare a Cadi (Chad) akan abinda suka ce. Wani ayari ne na 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai. Wataƙila da [unintelligible] hamɓarar da gwamnatin Cadi;
  2. Tarayar Turai ta ce masu sanya idanunta kan zaɓukan Najeriya za su je ƙasar, dukkuwa, da barazanar da gwamnan jihar Kaduna ya yi akan zuwan su. Ko ƙanƙani ba shi da nufin ya nemi a jima wani ko a hallaka wani ko ɗan Najeriya ko ɗan ƙasar waje dangane da harkar zaɓe. Magana ce yake yi da ta shafi kare kishin ƙasa da mutincin ƙasar sa ta Nigeria. --wakilin gwamnatin tarayya Garba Shehu;
  3. Sojan Zimbabwe sun ce sun kammala aikin da suka yi na samar da kwanciyar hankali da bin doka a ƙasar;
  4. Za mu ji wani mataki da gwamnatin Amurka ta ɗauka akan Kamaru.
Feb 07, 201901:28
DW Hausa - Shirin Safe na 07.02.2019
Feb 07, 201929:56
Buhari's UN Speech 2017-9-19

Buhari's UN Speech 2017-9-19

President Buhari's full speech at the 72nd UN General assembly
Sep 20, 201712:58
Kanun Labaran Hausa 2017-9-5

Kanun Labaran Hausa 2017-9-5

Sashen Hausa na Iran 1 na 2017-09-05 \u2022 Sashen Hausa na Iran 2 na 2017-09-05 \u2022 VOA Hausa Shirin Safe 0500 UTC na 2017-09-05 \u2022 VOA Hausa Shirin Hantsi 0700 UTC na 2017-09-05 \u2022 VOA60 AFIRKA:Masu Binci...
Sep 06, 201738:01
August 31, 2017

August 31, 2017

VOA Hausa Shirin Safe 0500 UTC • VOA Hausa Shirin Hantsi 0700 UTC • VOA Hausa Shirin Rana 1500 UTC • VOA Hausa Yau da Gobe 1530 UTC • VOA60 AFIRKA: A Dakar, Kotu Ta Saki Dan Gwagwarmayan Nan Kemi Seba • VOA60 DUNIYA: An Fara Gudanar Da Aikin Hajji Na Kwanaki Biyar A Mecca • Labaran Talabijin na 30/08/17 • VOA60 AFIRKA: Hukumomi Sun Ce Akalla Mutane 44 Sun Mutu A Nijar • VOA60 DUNIYA: Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Ya Caccaki Cibiyoyin 'Ya • Tawagar Dan Majalisar Dattawan Amurka Christopher Coons Ta Kai Ziyara Maiduguri • BBC Hausa Labaran Talabijin na 31/08/17 • BBC Hausa Labaran Shirin Yamma 31/08/17 • BBC Hausa Labaran Shirin Safe 31/08/17 • VOA Hausa Shirin Rana 1500 UTC • DW Hausa Shirin Safe 0630 UTC na 31/08/17 • DW Hausa Shirin Rana 1300 UTC na 31/08/17 • DW Hausa Shirin Yamma 1800 UTC na 31/08/17 • RFI Hausa 06h00 - 06h17 GMT Labarai 31/08 • RFI Hausa 07h00 - 07h17 GMT Labarai 31/08
Sep 01, 201725:12