Usman Kabara
By Usman Kabara
Usman KabaraFeb 17, 2023
KAMALUDDEEN KABIR: Yadda ya sami karatu a Birtaniya
Dakta Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.
NA’IMA IDRIS: Ta shiga sahun manyan gobe a Afirka
Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022.
SOJABOY: Bahaushen da Amurkawa suka fi sani
AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali
Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo. AISHA HASSAN: 'Yar Najeriya da Birtaniya gwanar daurin dan-kwali
HALIMA ALI SHUWA: ‘Yar Najeriyar da aka karrama a Birtaniya
An karrama Halima da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa’o’inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil’adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta.
MUA'WIYA SA'IDU: Dan Najeriya masanin tsara birane a Koriya ta Kudu
Mu'awiya Said Abdullahi, ya yi karatu ne a fannin zanen gidaje da kuma tsara birane. An haifeshi ne a garin Kaduna, sannan iyayensa Lauyoyi ne. Ya fara digirinsa ne daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya kuma kammala a daya daga jami’o’in kasar Malaysia. Yayi digirinsa na biyu da na uku a Korea ta Kudu, inda yanzu haka ya ke aiki a matsayin shugaban bangaren kula da bangaren tsara biranen kasashen waje a wani babban kamfani a kasar ta Koriya ta Kudu mai suna WithWorks da ke birnin Seoul.
I SHARIF: Dan Najeriya matukin jirgi a Afirka ta Kudu
Kaftin Ibrahim Sharif bakano ne dan Najeriya da ya bar gida tun yana dan saurayi zuwa Birtaniya domin aikin sa kai. Inda daga baya ya nausa Afirka ta Kudu inda ya cika burinsa na zama matukin jirgin sama, har ma ya buge da tsere keke a can.
NURA ABUBAKAR: Koyar da Hausa ya kai shi Amurka
MARZUQ UNGOGO - Likitan Dabbobi
Marzuq Ungogo wani hazikin matashin likitan dabbobi ne da yake digirin-digirgir a birtaniya, tare da yin binciken a fanni kwayoyin cututtukan dabbobin da kuma gano dalilan da ke hana wasu magungunan dabbobin aiki da ya kamata su yi. Ya bayyana mana tarihin rayuwarsa da ma yadda aka yi yayi digiri na biyu a Turai da ma ci gaba da digirinsa na uku. Ya tabo batun yadda yake ganin noma da kiwo a kasashe kamar Najeriya.
IMAN YUSUF AL-HASSAN - 'Yar Kimiyyar Lafiya
MAIMUNA SULAIMAN BICHI: Gwanar Girke-Girke
Maimuna Sulaiman Bichi da aka fi sani da ‘Yar Bichi ko Lolo’s Kitchen ‘yar asalin Najeriya ce ta suka dawo Amurka da zama tun tana shekaru 15 da haihuwa. Ta kuduri aniyar bude gidan abincin da zai kware a girke-girke musamman ma irin na gargajiyar Hausawa.
BINTA ALIYU ZURMI: ‘Yar Jarida
Binta Aliyu Zurmi da aka fi sani da Elbynt, ‘yar jarida ce daga Najeriya mazauniyar kasar Jamus kuma ma’aikaciya a daya daga fitattun gidajen radiyon Hausa da ke kasashen waje. Ku biyo mu don kallo ko sauraron tattaunawar da muka yi da ita game da tarihin rayuwarta a gida da kasahen waje.
MOHAMMED LADAN: Masanin Magunguna
An fi sanin Mohammed Ladan da sunan Dakta Ladan, sakamakon wani fitaccen shirin lafiya na gidan radiyon sashen Hausa na Muryar Amurka. Amma a likitance shi masanin kimiyyar hada magunguna ne wato ‘phamacist’. Dan asalin jihar Neja ne da ke Arewacin Najeriya, sannan a yanzu mazaunin Amurka fiye da shekara 40 tun bayan zuwansa karatu.
BELLO SHARIFF SISQO: Mawakin Hausa
Bello Sheriff Sicqo haifaffen Maiduguri ne amma girman Kano a tarayyar Najeriya, wanda ya ci karo da kalubalen rayuwa a dalilin basirarsa ta waka wanda har korarsa daga gidansu aka yi. Amma maimakon ya saduda, sai ma ya tsalleke kasar zuwa Jamus a tarayyar Turai inda a yanzu haka yake zaune a matsayin mawaki kuma mai koyar da rawai.
AISHA RIMI: Marubuciya
Aisha Rimi ‘yar kasar Birtaniya ce wacce iyaiyenta ‘yan asalin Arewacin Najeriya ne. Duk da fadawa hatsarin da ya yi sanadiyyar rabata da kafarta daya, to amma hakan bai canza komai a samun nasararta a rayuwa ba.
YUSUF AL-HASSAN: Farfesan Ilmin Sana'a
Yusuf Alhassan dan asalin cikin birnin Kano ne da ya kwashe shekaru yana koyo da koyarwa a tsakanin Najeriya da Amurka game da ilimin fasahar sana’o’in hannu inda har ya taba zama zakaran gasar malaman koyar da sana’o’i ta Amurka. Malamin ya kuduri aniyarsa ta yadda zai taimaki Najeriya ta hanyar kai Kanawa 100 zuwa Amurka don koyon ilimin sana’a.
ALIYU MUSTAPHA LAWAL: Gasar Larabci
Aliyu Mustapha Lawal bakano ne daga Najeriya wanda yake zaune a kasar Masira sannan ya shiga gasar kasidar larabci ta duniya mai taken Yariman Sha’iran Larabawa a birnin Abu Dhabi ta hadaddiyar daular larabawa. Ya tattauna damu game da rayuwarsa tsakanin Najeriya da Misira da kuma yadda aka yi ya sami shiga gasar larabawa a matsayinsa na bahaushe.
ABBA ZUBAIR CHEDI: Farfesan Kwayar Halitta
Farfesa Abba na asibitin Mayo Clinic da ke Amurka, dan asalin jihar Kano ne a Najeriya da ya yi kaurin suna a Amurka, musamman a lokacin da ya shiga binciken yadda za a yi amfani da kwayar halitta ta stem cell a Turance wajen kirkirar maganin da zai iya sabunta halittar sassan jikin bil adama kamar zuciya da huhu ko bargo da makamantansu don yi wa dan Adam dashe idan sassan jiki ya lalace.
HAUWA MUSTAPHA BABURA - Malamar Yara
Hauwa Mustapha Babura wacce ake mata lakabi da ‘Yar Babura sanadiyyar sunan garinsu Babura da ke jihar Jigawa a Najeriya, amma yanzu haka tana zaune a Amurka fiye da shekaru 30 wanda har ta zama ‘yar kasa. Mun tattauna da ita don ita don jin gwagwarmayar da ta sha kafin ta zama kwararriyar malamar makaranta a bangaren ilimin kananan yara da kuma yadda ake renon kwakwalwarsu.
SARATITIN BABA: Gwanar Aikin Jinya
MURTALA MAI: Gwanin Lafiyar Al'umma
FADJI MAINA: 'Yar Kimiyyar Kasa
‘Yar Nijar kuma masaniyar kimiyyar ruwa da doron kasa da ke aiki a hukumar sama-jannatin Amurka ta NASA. Dakta Fadji Maina tana cikin wacce mujallar tereren arziki ta Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasan duniya guda 30 ‘yan kasa da shekara 30 da suka sami nasara a rayuwa. Yanzu haka ma’aikaciya ce a hukumar sama jannatin Amurka ta NASA da ke aiki bisa kwarewar ta a fannin ruwa da kimiyyar doron kasa.
SARKI ABBA ABDULKADIR: Farfesan Kwayar Cuta
A shekarar 1984 a Najeriya an sami wani saurayi dan jihar Kano da ya fi kowane dalibi a Najeriya cin makin jarrabawar gama sakandaren kasashen Afirka ta WAEC a takaice. Yanzu haka dai wannan dalibin mai suna Sarki Abba Abdulkadir farfesa ne a bangaren haddasuwar cututtuka a Jami'ar Northwestern University da ke Chicago a Amurka.
ADAMU BAMALLI: Injiniyan Gine-Gine
IMRANA ALHAJI BUBA: Dan Gwagwarmaya
HALIMA DJIMROA: 'Yar jarida
SABO TANIMU - Likitan Hanji
HARUNA CHIZO1 - Sarkin Samarin Turai
A cikin wannan hirar ne mawaki kuma dan wasan barkwanci sannan Sarkin Samarin Turai mai suna Haruna Salisu da aka fi sani da Chizo1 Germany, ya fada mana tarihin rayuwarsa tun daga Najeriya zuwa shigarsa Turai a matsayin dan gudun hijira ta hanyar keta sahara da teku har da yadda ya tsinci kansa a kasar Jamus inda ya buge da auren Bajamushiya.
MADUBIN KABARA - Usman Kabara Show - Hausa
Ni Usman Kabara na kirkiro shirin nan ne don in dinga zakulo Hausawan da suka yi fice ko nasara a fannoni daban-daban a fadin duniya domin jin irin gwagwarmayar da suke sha kafin kai wa ga gaci, don hakan ya zama jagorar tinkarar rayuwa ga matasanmu. Ku lalubi shirin tare da danna 'subscribe' ko 'follow' a radiyon tafi da gidanka internet a tsarin ‘podcast’ dake kan man-hajar 'Apple Podcasts' da 'Google Podcasts' da 'Spotify' da duk inda kuke samun podcasts dinku.